ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto kakakin hukumar abinci da magunguna na kasar, Kianoush Jahanpour yana fadar haka a shafinsa na Tweeter, ya kuma kara da cewa yawan alluran sun kai 250,000 kuma za’a yi wa jami’an kiwon lafiya da wadanda suka ji raunin a yakin shekaru 8 da kasar Iraqi alluran.
Kianoush Jahanpour ya kara da cewa ya zuwa yanzu an yiwa mutane 110,000 alluran riga kafin cutar ta Korona, da alluran riga kafi na Sputnik V na kasar Rasha.
Banda haka masana a kasar Iran suna aiki tukuru don samar da alluran riga kafin a cikin gida, iri biyu, akwai Coviran Barakat da kuma Riza CoV-Pars wadanda suke marhala ta karshe na gwaje-gwajensu a kan mutane.
342/